Wednesday, November 11
Shadow

Kalli Bidiyon: Bikin Nuna Kwalliya ta mata da maza da diyar Sarkin Kano, Sabeera Sanusi ta shirya da ya jawo cece-kuce

Diyar me martaba Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II me suna Sabeerah Sanusi ta shirya bikin nunawa kawa na mata da maza watau fashion show.

Bikin ya dauki hankula inda aka ga maza da mata sun caba ado sun fito gaban jama’a suna ta rangwada, kamar dai yanda ake yi a kasashen Turai musamman kasar Faransa inda acanne aka fi yin irin wannan bukukuwan.

Shi kansa me martaba sarki ya samu damar Halartar wannan waje.

Wata data fi daukar hankali a wajan itace wadda data gama rangwadarta a gaban mutane saita cire siket dinta.

An ta bayyana mabanbanta ra’ayoyi akai inda wasu suka yaba, wasu kuwa cewa suka yi abin bai dace sa al’ada da addini ba.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna:Dan gidan Ministan Ayyuka, Osborn Umahi ya fito takarar kujerar shugaban karamar hukuma

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *