
Matar shugaban kasa, Remi Tinubu ta kunyata Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke yayin da yake jawabi a wajan taro.
Ta taso ta sameshi tace ta gaggauta ya kammala jawabinsa ta bashi mintuna 5 ya ishesu da wake-wake.
An ga ta gaya masa hakan cikin bacin rai tana nuna masa yatsa, kamar danta.
Bidiyon dai ya jawo cece-kuce inda wasu ke cewa bai kamata tawa gwamna guda haka ba.