
Wani Fasto Inyamuri ya bayyanawa shugaban kasar Amurka, Donald Trump cewa, zaman Lafiyar Kiristoci shine a raba Najeriya Kiristoci a basu jihohinsu, Musulmai a basu jihohinsu.
Yace jihohin musulmai guda 10 ne kacal a Najeriya, watau Katsina, Jigawa, Kano, Sokoto, Kebbi, Zamfara, Borno, Yobe, Adamawa, da Gombe.
Yace amma daga Kaduna abinda yayi sauran jihohin tsakiyar Najeriya zuwa kudancin Najeriya duk jihohin Kiristoci ne sai a raba a samusu sunan Biafra.