Friday, July 31
Shadow

Kalli Bidiyon Gaskiyar lamari kan kama Farouk Abuja me yawan sukar manyan mutane a shafinsa

Farouk Abuja dake yawan sukar manyan mutane a shafinsa na sada zumunta ya shiga hannun jami’an tsaro.

A baya dai an rika cewa an kamashi wasu basu yadda ba inda daga nan ne sai ga Bidiyon sa ya bayyana a kafafen sada zumunta a hannun jami’an tsaro.

Aminu J Town wanda shima sun taba Bugawa da Farouk Abuja ya bayyana cewa, Lauyan Ministan Tsaro Christopher Musa ne yasa aka kama Farouk Abuja saboda ci masa mutunci

Sannan yace dalili kenan da yasa shima wani babban soja da ya dade yana ciwa mutunci ya fito yake neman hakkinsa akan Farouk Abuja.

J town yace da ‘yansanda suka kama Farouk Abuja ya musu ihun wai sun saceshi ne bai san inda zasu kaishiba.

Karanta Wannan  Kalli Bidiyon: Mahaifinmu bai Rasu ba, ya koma wata rayuwane>>Inji Naziru Sheikh Dahiru Usman Bauchi

Saida suka tsaya sukawa mutane bayanin gaskiya akan Lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *