
An ga wani tsohon Bidiyon gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya na fadar wata magana da Kwankwaso yayi wadda bai ji dadinta ba.
Bidiyon dai tsohone amma yana ta yawo a kafafen sada zumunta.
An ji Abba yana cewa, Kwankwaso yace idan sun nemi shawara zai basu idan basu nema ba zai zuba musu ido.
Saidai Abban yace bai ji dadin wannan magana ba dan har sai da ya je ya samu Kwankwaso akan maganar.