
Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Fintiri ya baiwa Kocin kungiyar kwallon kafa ta mata ta Najeriya, Super Falcons, Justin Madugu kyautar gida da Naira Miliyan 50.
Ya bashi kyautar ne a gidan gwamnatin jihar Adamawa.
Ya bashi kyautar saboda kokarin da yayi na kai ‘yan matan suka lashe kofin Afrika na mata wanda suka buga wasan karshe da kasar Morocco.
Suma dai ‘yan matan kowacce gwamnatin tarayya ta basu kyautar Naira Miliyan 152 da kuma gidaje.
Sannan gwamnoni sun basu kyautar Naira Miliyan 10 kowacce.