
A karshe dai Tauraron Tiktok, GFRESH Al-amin ya hadu da Sheikh Ibrahim Maqari inda yace ya ji nasihar da malam ya masa.
Gfresh yace zai rika fadakarwa yanzu ko da ta hanyar wasa ne.
A jiya ne dai aka ga Gfresh a gaban malam yana tambayar shin ko ya halatta mutum ya rika Bidiyo da iyalinsa yana watsawa Duniya.
Malam dai ya bashi Amsar cewa, idan abinda ake yi bai sabawa addini ba, babu matsala.