
Malam Dr. Hussain Kano ya sake tabbatar da maganarsa cewa baya son Allah ya kaishi matakin da sai ya nemi ceton Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) kamin ya shiga Aljannah ranar Qiyama.
Ya bayyana cewa masu sukarsa basu san Addini da kyau bane.
Yace aiki shine ke sanadin a saka mutum a Al-jannah amma mutum ya saki jiki yana sharholiya yana tunanin Manzon Allah SAW zai ceceshi ba daidai bane.
Yace duk wanda kaga Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ya ceceshi to Fajirine, Ladarsa bata kai yawan da zata shigar dashi Aljannah ba.