Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyon inda Amaechi yake cewa su ‘yan siyasar Najeriya sun san da wahalar da talakawa ke ciki amma ba ta damesu ba kuma ba zasu daina satar kudin talakawa ba

Tsohon Gwamnan jihar Rivers kuma tsohon Ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya bayyana takaicinsa game da yanda Talakawa ke tsammanin wai shuwagabanni zasu gyara halinsu.

Yace dole sai an yi juyin juya hali wanda kuma yace bai samuwa cikin sauki dole sai an zubar da jini.

Amaechi yace dukansu basu wuce mutane tsakanin dubu 20 zuwa dubu 100 ba amma gashi mutane miliyan 200 sun barsu sai gasa musu aya a hannu suke.

Yace korafi da shirya taruka ana ta kokawa kan satar shuwagabanni ba zai sa su daina satar kudin gwamnati ba.

Amaechi yace in ba talaka tashi yayi tsaye ya kwatarwa kansa ‘yanci ba, babu wani gyaran da za’a samu.

Karanta Wannan  Muna kokarin ganin kowane gida ya wadata da abinci>>Shugaba Tinubu

Amaechi ya bayyana hakane a wajan wani taron siyasa da aka gayyaceshi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *