
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya bayyana cewa, ya mayar da matarsa, Sadiya Haruna bayan rabuwarta da Best Choice.
Ya bayyana hakane a wani Bidiyo da ya wallafa inda yace amma Sadiya tace kada ya gayawa kowa.
A wani Bidiyonsa kuma, An ga Gfresh da Amaryarsa ‘Yar Yola inda yace tana fushi wai dan ya dawo da Sadiya Haruna.
Ya gaya mata cewa, iyayensu suna da Kishiya, Hakuri ake yi.
Tuni dai Sadiya Haruna ta bayyana cewa ta yi aure amma bata bayyana wa ta aura ba.