Monday, October 5
Shadow

Kalli Bidiyon: Ka rika shan ruwan Alwala ko Zuciyarka ta yi sanyi>>Sheikh Salihu Zaria ya gayawa Dr. Jamil bayan ya sokeshi saboda kaiwa Dr. Junaid ziyara

Sheikh Salihu Zaria ya mayarwa da Dr. Jamil Dutsen Tanshi Martani bayan da ya gaya masa cewa, bai kamata ziyarar da ya kaiwa Dr. Junaidu ba.

An ga Shaikh Salihu Zaria ya kaiwa Dr. Junaid ziyara har masallacin da yake karatu inda shima yayi fadakarwa.

Saidai Dr. Jamilu yace wannan ziyara bata dace ba dan ga Ahlussunah nan da yawa a Bauchi, Malam bai kai musu ziyara ba sai Dr. Junaid.

A martaninsa, Sheikh Salihu Zaria yace ya gode da kiran ya ji tsoron Allah da Dr. Jamilu ya masa yace amma ya rika shan ruwan alwala ko zuciyarsa ta yi sanyi.

Karanta Wannan  Kalli Hotuna:Yanda aka ceto wata Budurwa da saurayi ta ya mata tsìràrà ya daureta dan yin tsafi a dakin Otal

Yace kuma shi baya boye akidarsa ko ina yaje shi Dan Izala ne sannan kuma Najeriya ce ta hadasu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *