
Rahotanni sun bayyana cewa, Kasar Saudiyya ta gayyaci tsohon Hadimin shugaban kasa, Malam Bashir Ahmad zuwa sakawa dakin Ka’aba Turare.
Malam Bashir Ahmad da kansa ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ta shafinsa na sada zumunta inda ya bayyana cewa wannan ba karamin karramawa bace a gareshi.
Tsohon Ministan sadarwa, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami ya taya Malam Bashir Murna inda yace yana fatan Allah ya karbi wannan abu a matsayin Ibada ya bashi lada.