
Wani gidan Alfarma wanda babba ne sosai da aka dauki Bidiyon sa aka yada a kafafen sada zumunta aka ce gidan limamin Masallacin Harami, Abdulrahman Al-Sudais ne ya dauki hankula sosai.
An ji wata murya a cikin Bidiyon da aka dauka a garin Makkah na fadar hakan.
Wasu sun rika sukar Sudais da cewa, bai Nuna Zuhudu ba, Saboda magabata basu yi fariya da Dukiya haka ba
Inda wasu ke cewa, Ai ya cancanci gidan da ya fi wannan kyau ma.
Saidai wasu sun karyata wannan ikirari inda suke cewa gidan Yarima Sultanne.