
Golan Senegal Yehvan Diouf wanda ke wajan fili yayin da ake wasa, ya rikewa bokin aikinsa tsumman goge zufa ya hana ma’aikatan Filin wasan daukarsa.
A wani Bidiyo da ya karade kafafen sada zumunta, an ga golan yana kokawa da ma’aikatan filin yayin da suke ta kokarin kwace tsumman daga hannunsa.
A baya dai, An ga yanda ma’aikatan filin suka dauke tsumman na goge zufar golan Najeriya, Nwabali wanda hakan ya jawo cece-kuce sosai.