
‘Yar kasuwa, Laila Uthman tace zata saka ‘yarguda dake Tiktok tare da Maiwushirya a makaranta.
Ta bayyana hakane a wajan wani biki data hadu da su biyun.
An tambayi ‘yarguda ko tana son komawa Makarantar? Ta amsa da cewa Eh.
Saidai Sujadar Godiya da ‘Yarguda da Maiwushirya suka yi bayan hakan ta jawo cece-kuce.
Sujadar dai ta godiya ga Allah ce amma da yawa sun fassarata da wani abu daban.