
Wannan wani matashine dan Arewa dake yankan Farce a Lagos da irin ‘yan iskan gari dinnan da ake cewa Street Boys ya tareshi.
Yace masa sai ya biya kudin Haraji amma matashin yaki.
Lamarin yayi kamari tsakaninsu inda har ya eika ja mai jakar aikinsa.
Bidiyon ya watsu a kafafen sada zumunta inda ake ta Allah wadai da dan iskan.