
Wani matashi dan Najeriya ya jawo cece-kuce sosai a kafafen sada zumunta saboda kwace duk wata kyauta da ya taba yiwa Budurwarsa bayan rabuwarsu.
Lamarin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta inda wasu suka goyi bayanshi wasu kuma suka ce be kyauta ba.
Saidai a martaninsa yace Allah ma ya fitar da Annabi Adamu da Hauwa daga Aljannah bayan da suka saba masa.