A yau, ɗaya daga cikin manyan burina ya cika na Siyawa Babana sabuwar mota. 🚘❤️ Alhamdulillah! 🤲❤️ Tun da dadewa nake mafarkin ganin iyayena cikin farin ciki, kuma samun damar yin wannan abu a gare su ni’imar Allah ce da ba zan taɓa ɗauka da wasa ba. Iyaye ba su da madadi. Duk abin da muka mallaka a rayuwa, babu abin da ya fi darajar ganin mahaifi da mahaifiya cikin farin ciki, lafiya da kwanciyar hankali. Duk abin da za mu iya yi musu, mu yi tun suna tare da mu. Domin wata rana za mu yi kewar damar da muke da ita a yau. Ya Allah, Ka tsawaita wa iyayena rai cikin lafiya da imani, Ka ba ni ikon ci gaba da faranta musu rai, Ka saka musu da mafificin alheri bisa dukkan wahala da sadaukarwar da suka yi a kaina. 🤲 Alhamdulillah for this blessing. ❤️ Burin da na dade ina fata ya zama gaskiya. Alhamdulillah. 🙏❤️