
Gwamnatin tarayya tace Mintuna 5 kamin harin da Amurkar ta kai Sokoto, ta yi magana da Amurkar kuma a amince.
Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya bayana hakan.
Yace yayi magana da jami’in hulda da kasashen waje na kasar Amurka, Marco Rubio inda yace masa suna neman izinin kawo hari Najeriya.
Sai yace masa zai nemi Izini wajan shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu, kuma shugaban kasar ya amince da kai harin.
Yace sun dade suna neman yin aiki tare da kasar Amurka dan magance matsalar tsaron Najeriya.