
Wannan wata ‘yar Najeriya ce da ta je aikatau kasar Saudiyya.
Ta bayyana cewa a baya tasha duka Larabawa masu kudi ne.
Tace amma da ta je sai ta ga akwai wanda ko isashshen abinci basu dashi.
Tace gidan da aka kaita aiki har satar mata taliya ‘yar Hausa suke idan ta dafa ta ajiye.
Tace tana fatan dai Allah yasa kudin aikin ta su fito.