
Wani matashi daga jihar Bauchi ya aikawa Bulama Bukarti tambaya da neman shawara kan abinda ya kamata yayi bayan da ya gano cewa, Budurwar da zai aura malaminta na jami’a yana aikata Alfasha da ita.
Bulama ya bayyana hakane a Tiktoklive da yake yi da sauran wasu masu sharhi.
Yace a dokar Najeriya babu Soyayya takanin malami da dalibarsa.