
Shahararren fasto dake yawan sukar Musulunci da musulmai, Rev. Ezekiel Dachomo ya bayyana cewa, a baya shi tsohon dan fashi da makami ne.
Yace a shekarar 1980 sun taba zuwa suka yi fashi a wani banki a jos.
Yace amma Jesus ya sameshi da mala’iku 7 yace ya yafe masa zunubansa sannan kuma ya shiryeshi.
Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi a kwanakin baya wadda ta dauki hankula sosai.