Friday, December 5
Shadow

Kalli Bidiyon tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai yana fadin cewa Gwamnatin Tarayya tana Baiwa tshàgyèràn Dhàjì kudi da kayan Abinci, inda yayi zargin cewa Jihar Kaduna Biliyan 1 ta basu

Tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya yi zargin cewa hanyar da Gwamnatin yanzu ta dauka itace ta baiwa tsageran Daji kudi da kayan abinci wai dan a rika lallabasu kada su rika kai hare-hare kan al-umma.

Yace jihohi da yawa na Arewa na kan wannan tsarin ciki hadda jihar Kaduna.

Malam ya kara da cewa a jihar Kaduna Naira Biliyan 1 aka baiwa tsageran dajin.

Yace suna da hujjoji akan hakan kuma idan lokaci yayi zasu fitar dasu.

Malam ya bayyana hakane a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV.

Karanta Wannan  Nuhu Ribadu na son zama shugaban kasa a 2031 bayan Tinubu ya gama shiyasa yake son bata min suna>>El-Rufai

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *