Thursday, October 1
Shadow

Kalli Bidiyon: Wannan Kiristar na ta shan yabo a wajan Musulmai

Wannan wata matashiyar Kirista ce data yi abin a yaba inda Musulmai da yawa ke jinjina mata.

Tana aiki ne d wani kamfanin jirgin sama ind wani Musulmai yaje ta duba masa kayansa zai je aikin Umrah.

Saidai jakunkunansa biyu ne, inda yace amma daya za’a saka masa a bayanansa inda yace ta saka dayar jakar tasa akan sunan wani.

Saidai tace mai bata yadda ba.

Yace mta shifa an saba mai haka.

Yace mata zai sallameta inda a cikin Bidiyon an ji yana ce mata ta bashi lambar asusun wayarta ya tura mata da cin hanci.

Duk da haka Tace gaskiya ita ba zata yi ba, tace bata san menene yake a cikin jakar tasa ba watakila kayan laifine ya dorawa wani a kamashi.

Karanta Wannan  A lokacin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan an min tayin Naira Miliyan 80 in tallatashi amma naki yadda>>Inji Ali Jita

Tace kuma ita kamfaninsu bsa irin wannan abin.

Wannan gaskiya data nuna yasa Musulmai da yawa suna jinjina mata yayin da suke Allah wadai da me zuw Umran.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *