
Wannan wani matashi ne dan bautar kasa daga kudancin Najeriya da yayi bautar kasarsa a jihar Bauchi kuma ya karbi Musulunci.
Bayan ya koma garinsu, ‘yan uwansa sun ga yana sallah shine suke ta mamaki suka ce ya bar gida a matsayin Kirista amma yanzu gashi Ya musulunta.
Sun daukeshi Bidiyon inda suka wallafashi a shafukan sada zumunta wanda hakan ya jawo muhawara.