
Jagoran tafiyar Kwankwasiyya, Dr. Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa shi fa bai ce ba zai koma APC ba.
Yace amma kamin ya koma sai an gaya masa me za’awa Talakawa.
Sannan sai an gaya masa shi wane matsayi za’a bashi.
Sannan sai an gaya masa matsayin gwamnatin jihar Kano da ‘yan majalisarsu.
Yace amma har yanzu babu wani da ya sameshi akan hakan.