
Ministan babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike yayi martani game da neman a saukeshi daga mukaminsa.
Yace masu kiraye-kirayen su kwantar da hankalinsu wanda ya nasashi ne ke da wannan ikon, idan yaga cewa baya aikata abinda ya dace, to shine zai saukeshi.
Ya kara da cewa amma shi yasan yana yin abinda ya kamata a matsayin Ministan Abuja.