
Daya daga cikin sojoji 11 da kasar Burkina Faso ta kama tsawon kwanaki 9 bayan da jirginsu ya sauka a kasar yace, jirgin nasu da gaske tangarda ya samu.
Ya bayyana hakane yayin ganawarsa da wakilan Najeriya ta tura kasar dan a baiwa shugaban kasar, Ibrahim Traore hakuri ya sakesu.
Ministan harkokin kasashen waje, Yusuf Tuggar ne ya jagoranci tawagar.