
Wani magidanci a jihar Katsina ya hau saman Katanga ya ki saukowa bayan da surukansa suka je gidansa suka dauko matarsa zuka tafi da ita.
Yace ba zai sauko daga saman katangar ba sai an dawo masa da matarsa.
Lamarin ya faru ne a Sabuwar Kofa, Katsina ranar Lahadi.
Da farko dai an rika yada cewa barawone bayan da Bidiyon ya yadu sosai a Katsina.
Amma daga baya kafar Katsina Daily News ta samo labarin ainahin abinda ya faru.