
A jiyane dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya je babban masallacin Juma’a na Abuja inda yayi Sallar Juma’a acan.
Saidai bayan kammala sallah yayin da zai bar masallacin, an ga yanda matasa suka masa ihun bama yi hadda ruwa duwatsu.
A Bidiyon dake ta yawo a kafafen sada zumunta, An ga matasan na dukawa suna daukar duwatsu suna fadar bama yi suna jefawa motocin shugaban kasar.
Saidai a martanin fadar shugaban kasa, Me magana da yawun shugaban kasar, Bayo Onanuga ya musanta cewa hakan ta faru inda ya wallafa wani Bidiyon da yake ikirarin cewa, Shewar jinjinawa akawa shugaban kasar a masallacin na Abuja ba ihun bama yi ba da jifa.