
A yau a hukumance, Sanata Natasha Akpoti ta kunyata kakakin majalisar dattijai, Sanata Godswill Akpabio inda ana zaune a majalisar ta tashi tsaye ta gabatar da korafinta na cewa ya nemi yin lalata da ita.
Tace tana gabatar da korafin take mata hakkinta da neman yin lalata da ita da kakakin majalisar yayi. Tace idan za’a iya tunawa a Gidan talabijin na Arise TV ta yi wannan zargi.
Tace to yau gashi ta kawo a hukumance tana zargin kakakin majalisar.
Bayan ta gama jawabinta, ta nemi kakakin majalisar ya bata umarnin gabatar masa da takardar zargin, inda yace ya bata umarni.
Haka ta taka tinkis-tinkis ta je gaban sandar majalisar ta rusuna sannan ta ajiye takardar korafin a gaban kakakin majalisar.
Ya bayar da umarnin a mikawa kwamitin ladaftarwa na majalisar da takardar korafin.