
Babban malamin addinin islama, kuma tsohon ministan sadarwa, Sheikh Farfesa Isa Ali Pantami ya fashe da kuka yayin da yake bayar da tarihin Yakun Uhud.
Saidai lamarin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta.
Wasu sun rikawa malam shaguben cewa da yana kan mulki rike da mukamin minista ya daina kuka inda wasu suka rika cewa yanzu da babu mukamin shine kukan nashi ya dawo.
Malam dai ya shahara wajan yin kuka saboda shauki yayin wa’azinsa.