
Lamarin ya farune a kasar Faransa inda wani matashi dan shekaru 20 wanda kirista ne amma ya shiga masallaci yace shi sabon shiga addinin Musukunci ne kuma yananson Limamin Masallacin ya koya masa yadda ake Sallah.
Ko da Limamin ya tashi yana Sallah, sai da ya bari ya yi sujada, ya zaro wuka ya caka masa fiye da sau 40.
Sunan Limamin Aboubakar Cissé kuma dan Asalin kasar Mali ne. Lamarin ya farune ranar 25 ga watan Afrilun da ya gabata.