Mutanen unguwar Jaen a Kano sun koka da ayyukan ‘yan daba inda suka nemi daukin Gwamnati kan lamarin.
Wani Bidiyo da ya watsu a shafukan sada zumunta ya nuna yanda matasan ke cin karensu ba babbaka a unguwar.
A shekarun baya dai jihar Kano ta yi fama da ayyukan ‘yan daba inda suka lafa amma da alama lamarin zai dawo danye.