
An kama karamin sojan Najeriya me suna Private Yahaya Yunusa a Jaji dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna saboda zargin safarar makamai.
Sojan dake aiki a bataliya ta 197 dake jihar Zamfara an kamashine ranar Juma’a da misalin karfe 11:55 a.m. inda aka samu albarusai 214 a wajensa.
An kuma kamashi da ATM da yawa.
Ya amsa laifinsa inda yace ya saci albarusanne daga wajen aikinsa dan shine ke kula da bindigar A.A da ake kafewa a bayan motar yakin sojoji.