An kama wannan matar me suna Temitope Adetanju ‘Yar Kimanin shekaru 25 saboda turawa karamar yarinya me shekaru 12 icce cikin farjinta.
An zargi yarinyar ne da satar Biskit na Naira 200 da Milo na 150 sai kayan marmari na Naira 300.
Rahoton yace an azabtar da yarinyar sosai saboda wannan zargi.
Lamarin ya farune a Isewo, Obada Oko, dake karamar hukumar Ewekoro na jihar Ogun.
Kakakin ‘yansandan jihar, Omolola Odutola ta tabbatar da faruwar lamarin inda tace wadda ake zargin ta amsa laifinta amma suna ci gaba da bincike.