Wednesday, January 15
Shadow

Kalli Hoton matar da aka kama da harsasai 2000 zata kaiwa ‘yan Bindiga a jihar Zamfara, da kuma wasu ‘yan Boko Haram da suka tuba

Wannan matar an kamata da harsasai 2000 zata kaiwa ‘yan Bindiga a jihar Zamfara.

Jami’an tsaron sun kamata ne da makaman amma babu cikakken bayanan me ya faru.

Hakanan wasu ‘yan Boko Haram, Baana Duguri, Momodu Fantami, Abubakar Isani da Zainami Dauda sun mika kansu wajan jami’n tsaro inda suka ce sun tuba.

 An kwace makaman Bindigar Ak47 guda 2, da Harsasai masu yawa, da wasu kananan bamabamai da mashina 2, da dai sauransu.

Sun bayyana cewa, sun fito ne daga garin Damboa.

Karanta Wannan  Kalli Hotunan wata maboyar 'yan Bin-di-ga da 'yansanda suka gano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *