An kama wannan mutumin me suna Malam Bala Abubakar a jihar Sokoto bayan samunaa da laifin sayar da yara har guda 28.
Wani abin mamaki ma shine cikin yaran da ya sayar hadda ‘ya’yansa guda 6.
An dai yadda da Malam Bala Abubakar a matsayin me kula da marayu.
Hukumar ‘yansanda ta jihar Sokoto tace yana sayar da yaranne ga wasu mata Elizabeth Oja da Kulu Dogonyaro da sunan za’a kai yaran Abuja dan wani mutum ya rika basu kulawa me kyau.
Malam Bala dai yana zaunene a unguwar Tudun Wada dake jihar Sokoto.
Kuma wanda suka sanshi sun yi mamakin abinda ya aikata.
Lamarin dai yana hannun ‘yansanda inda ake ci gaba da bincike.