
Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA ta sanar da kama wata mata ‘yar kasar Thailand me suna Ms. Pattaphi Wimonnat data shigo da Wiwi Najeriya.
An kama matar ne da akwatuna 43 na kwayar inda ta amsa laifinta da cewa wasu ne suka dauki hayarta suka ce idan ta kawo kwayar Najeriya zasu bata dala $3000.
Saidai gashi dubunta ya cika.