Sunday, July 13
Shadow

An kama mutane 2 a jihar Borno saboda Kkashe wata mata bisa zargin Maita

‘Yansanda a jihar Borno sun sanar da kama mutane 2 bisa zargin kisan da sukawa wata mata me shekaru 70 a Biu dake jihar bayan zarginta da maita.

Kakakin ‘yansandan jihar, CP Yusuf Lawan ya tabbatar da faruwar lamarin a sanarwar da ya fitar ranar Asabar, 22 ga watan Fabrairu 2025.

Ya bayyana sunayen wadanda ake zargi kamar haka,Ja’o Muhammad, Idrisa Muhammad, 20, da Ya’u Muhammad, 30. 

Yace matar sunanta Hajara Saleh wadda aka kashe a Bantine dake Biu.

Hukumar ‘yansandan tace mutanen da ake zargin sun hada kai dan kashe Hajara inda suka zargeta da maita da jawowa garinsu bala’i.

Ya bayar da tabbacin hukunta wadanda ake zargin.

Karanta Wannan  Lalacewar wutar Lantarki:Majalisa ta gayyaci ministoci dan binciken yanda aka yi da Dala Biliyan $2 da aka bayar da samar da wutar Lantarki

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *