
Gagga-gaggan ƴan bindiga 5 da rundunarsu a yankin Jibia sun tuba sun aje makami sun ayyana ba za su kara kai hari ba
Sun kuma mika bindigar AK49 har guda biyu don tabbatar da tubansu
An kai ƙarshen zaman tattaunawa tareda da tubabbun yan dindiga a karamar hukumar Jibia ta jahar Katsina.
A ranar Juma’a 28/2/2025, ne aka kai ƙarshen zaman tattaunawa da yan dindigar da suka shirya karɓar zaman lafiya a karamar hukumar Jibia a jihar Katsina.
Anyi zaman a karkashin jagorancin Chairman na karamar hukumar Jibia da Jibiya Peoples Froum da (NCSOSACK) da rundunar sojin Nigeriya ta jihar Katsina, daga cikin tubabbun yan dindigar da a kayi zaman tattaunawar dasu akwai.
1- Audu Lanƙai
2- Kantoma
3- Ori
4- Tukur Dan Najeriya
5- Bammi.
A yayin zaman an tattauna batutuwa da da dama da kuma shimfiɗa wasu sharuɗa wanda mutane garin na Jibiya suka gindayawa tubabbun yan dindigar.
Acikin sharuɗa da aka kafa musu sune:
1- Daina kai harere a acikin garin Jibiya da kuma kowanne ƙauye dake a ƙarƙashin karamar hukumar ta Jibia, da kan hanyar Jibia zuwa Katsina da kan hanyar Jibia zuwa Gurbi da kuma kan hanyar Jibia zuwa Batsari.
2- Barin kaiwa mutane hari a cikin gona ko daji tareda kiyaye gudu da babura acikin garin da kuma rashin tarbiya.
3- Kiyaye ɓarna acikin gonakan manoma
4- Kiyaye kowacce iriyar dokar da hukuma ta tanadar kamar yacce sauran al’ummar suke kiyayewa.
A nasu ɓangaren suma tubabbun yan dindigar sun bada nasu sharuɗa:
1- Daina kashe su ko kama su ko dabbobin su babu dalili
Tabbatar da adalci a tsakanin su da sauran al’umma a matsayin su na yan ƙasa
3- Daina ɗaukar doka a hannu/ Barin hukuma tayi hukunci ga duk wanda aka samu da laifi.
Tubabbun yan dindigar sun sake mutum goma waɗanda su kayi garkuwa dasu yan garin Ɗaddara, tareda bada bindiga kirar AK49 guda biyu.
Muna fatan Allah yasa wannan masalaha ta silar samun dauwamamen zaman lafiya a yanki mu da jihar mu da kuma kasar mu gabaɗaya.
28/2/2025,
Comrade K SBabah,
Project Manager NCSOSACK.