
‘Yansanda a jihar Enugu sun sanar da gano kokon kan mutum a wani kango inda aka ginin wata coci.
Ana zargin faston cocin da ake kira da Chinedu Solomon Ezedike yana amfani da sassan jikin dan Adam wajan gudanar da tsafi.
An gano hakan ne bayan binciken hadaka wanda aka yi da DPO din ‘yansanda na karamar hukumar Igbo-Eze dake jihar.
A baya dai an zargi faston da kashe wasu mutane 4 ‘yan uwan juna wanda ake zargin yayi amfani dasu ne wajan aikata tsafi.
Shugaban karamar hukumar, Barrister Ferdinand Ukwueze ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace jami’an tsaro sun kai samame wajanne bayan samun bayanan sirri.
Rahoton yace ana kan ci gaba da binciken lamarin.