Tuesday, November 18
Shadow

Kalli Hotuna yanda aka gano Kòkòn kàn mùtùm a cocin wani fasto da ake zargi da yin tsàfì da sàssàn jìkìn mutane

‘Yansanda a jihar Enugu sun sanar da gano kokon kan mutum a wani kango inda aka ginin wata coci.

Ana zargin faston cocin da ake kira da Chinedu Solomon Ezedike yana amfani da sassan jikin dan Adam wajan gudanar da tsafi.

An gano hakan ne bayan binciken hadaka wanda aka yi da DPO din ‘yansanda na karamar hukumar Igbo-Eze dake jihar.

A baya dai an zargi faston da kashe wasu mutane 4 ‘yan uwan juna wanda ake zargin yayi amfani dasu ne wajan aikata tsafi.

Shugaban karamar hukumar, Barrister Ferdinand Ukwueze ya tabbatar da faruwar lamarin inda yace jami’an tsaro sun kai samame wajanne bayan samun bayanan sirri.

Karanta Wannan  Likitoci a Najeriya sun janye yajin aikin gargaɗi

Rahoton yace ana kan ci gaba da binciken lamarin.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *