Rahotanni daga Bassa da Erena a jihar Naija na cewa mayakan kungiyar B0k0 Hqrqm sun kai mummunan hari a yankin.
Majiyar Hutudole tace an kai harinne a garin Makuba Lantan Bakin Kogi Bassa inda aka kashe mutane 7 ta hanyar yi musu yankan rago.
Harin ya farune a jiya, Alhamis kamar yanda majiyar tamu ta tabbatar.
Masu fada a ji a yankin sun nemi mahukunta da su kaiwa mutanen yankin musamman wadanda suka rasa muhallansu dauki.
Mun samu hoton kan daya daga cikin mutanen da aka yanke, Allah ya kyauta.