
Rahotanni daga jihar Kaduna sun bayyana cewa, ‘yansanda sun kulle ofishin jam’iyyar ADC a jihar yayin da kungiyar ke shirin gudanar da taro.
Wasu daga cikin ‘yan jam’iyyar sun hau kafafen sada zumunta suna bayyana mamaki da rashin jin dadinsu.
“”An Jibge Jami’an Tsaro Sama Da Mota 20 Domin A Hanamu Taron Da Zamuyi Ayau” A Ofishin Jami’iyyar ADC Dake Kan Titin Ali Aƙilu.
Wacce irin siyasa akeyi haka a jihar Kaduna?, anata amfani da jami’an tsaron da’aka samar domin tsare ƙimar Demokraɗiyya ana yiwa Demokraɗiyyar fyaɗe. sannan a turo wasu wanda basufi ƙarfin cikinsu ba, wanda da ƙyar suke iya biyan kudin haya, suzo media suna kare ƙarya da zalunci.
Ance an kashe adawa a jihar Kaduna, to kenan me ake tsoro tunda an kashe adawa?, Allah ya kyauta” Inji Comrades DanHabu
“”An Jibge Jami’an Tsaro Sama Da Mota 20 Domin A Hanamu Taron Da Zamuyi Ayau” A Ofishin Jami’iyyar ADC Dake Kan Titin Ali Aƙilu.
Wacce irin siyasa akeyi haka a jihar Kaduna?,” inji Aisha Galadima.