Hotunan tashar jirgin kasa ta zamani da ake ginawa a Kano sun dauki hankula.
Tsohon Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ne ya fara aikin gina tashar wadda titin jirgin zai tafi har cikin kasar Nijar dan saukaka tafiye-tafiye da kasuwanci.
Bayan kammala aikin ginin tashar ana sa ran zata taimaka matuka wajan samar da ayyukan yi.