
Sanata shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattijai a shekarar 2015 zuwa 2019 ya sha raddi a kafar X.
An wallafa wani Bidiyo ne inda aka nuna mata tsirara daga su sai dan kamfai a wani shagon Aski da aka ce a Najeriya yake auna rawa.
Da yake bayyana ra’ayinsa akan bidiyon, sanata Shehu Sani yace ka zo Najeriya zaka ga abubuwan ban mamaki.
Saidai da yawa sun yi mamakin ganin comment dinsa a kasan Bidiyon ganin cewa bidiyon na dauke da tsiraici.
Da yawa sun rika tambayar anya Sanata Shehu Sani na Azumin kuwa?