
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya raka gawar kawunsa, Aminu Dantata daga Abu Dhabi kasar UAE zuwa Birnin Madina na kasar Saudiyya.
Aminu Dantata ne daya daga cikin kawun Dangote Dangote na karshe da suka rage masa.
Bayan sallar la’asar a kasar Saudiyya da misalin karfe 1:30 a Najeriya ne za’a yi jana’izar Marigayin.