
Wata mamakon gobara ta barkena tsakiyar kasar Israyla inda take ta yaduwa sosai.
Gobarar da ba’a san inda ta samo Asali ba ta tashine a birnin Ness Ziona kuma ‘yan kwana-kwana na ta kokarin kasheta.
Rahotanni sun ce an tattaro ma’aikatan kwana-kwana daga yankuna daban-daban dan su taimaka a kashe gobarar.
Hukumomi sun ce Tuni aka fara kwashe mutane daga gidajen da Gobarar ta durfafa.