
Kamfanin sadarwa na Airtel ya sanar da tafka asarar Dala Miliyan $344 a wajan kasuwancin sayar da data.
Kamfanin yace ta tafka asarar a watanni 9 da suka gabata wanda suka kare a karshen watan Disamba na shekarar 2024.
A shekarar baya kamfanin ya samu kudin shiga daga kasuwancin sayar da data wanda suka kai dala miliyan $539.
Hakan na faruwane yayin da yawan masu amfani da layin waya na Airtel suka karu wanda a yanzu sun kai Mutane Miliyan 56.6.
Shugaban kamfanin, Dinesh Balsingh ya bayyana cewa suma sun kara kudin kira dana data dan samu su ci gaba da inganta ayyukansu kamar yanda takwarorinsu irin su MTN suka yi.